Old school Easter eggs.
Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
Wannan 6angare InshaAllahu ze dinga zuwa muku ne daga y'ar uwar ku,
Malama Ummi Ahmad Katsina
Kuna Iya Binta ta shafin Face book
Wanda ya tsara kuma ya shirya,
Basheer Journalist Sharfadi


TARBIYYA VOL 1.
.
Tarbiyya -Itace halayya ko dabi'un masu kyau da kowace kowace kabila da jinsi take da nata tsarin.
.
Tarbiyya takunshi abubuwa daban daban Misali mu muslmai kuma hausawa tsarinmu zan iya cewa shine babban tsari.
.
Idan kuka duba duk yaron bahaushe da zai taso cikin tarbiyya mai kyau zakusame shi,abin sha'awa ga kowa.
.
Anan zandakata sai Allah yasake sadamu .



TARBIYYA VOL 2.
.
TAYA ZAMU TARBIYYANTAR DA YARANMU?
.
Icce tun yana danye ake tankwasashi.Dazarar yaronka ya fara gane abu (misali yanada sheka ra biyu) in kinwa taro tsawa kikan firgita shi Ku ma dazarar ya firgita zakiga ya daina abinda a
binda yakeyi. To yana kara girma da wayo kiriniya tana karuwa,dan haka yar'uwa sai kinyi aiki sa nutsuwa,da kulawa sosai akan yaranki.a
.
anan zandakata sai Allah yasake hadamu.



TARBIYYA VOL 3.
.
BA'A TARBIYYA DA DUKA!
.
Idan yaronki yayi maki laifi,kirashi kizaunar dashi agabanki. Kice yanzu Muhammad abi nda kayi ka kyauta kenan?
.
kanaso muyi fushi dakai?
.
Allah baya son abu kaza da kaza da kakeyi.
.
Kina masa nasiha kina gaya masa illolin abin tare da tsoratar dashi. misali,
.
Inka yi kaza Allah zai soka kuma zaibaka lada.
.
Yasaka a aljanna,kaza da kakeyi Allah baya so kuma zaiyi fushi da kai,kadainayi Kaji muhammad a karshe kace Allah yayi maka Albarka,
.
Duk lokacinda yaronka ya bata maki rai kiyi hakuri kada kibishi da muna nan kalamai ko duka,duka bazai kareki da komaiba sai ka rin bacin rai.
.
Anan zandakata Sai Allah ya hada mu a shiri nagaba.



Ummi Ahmad wrote a new note: TARBIYYA VOL 4.
.
SALLAMA.
.
Ki koyawa yaranki SALLAMA kodaga daki suka fito zuwa falo inbasuyi sallama ba ki ce meyasa suka shigo basu yi sallama ba?
.
kice sukoma suyi sallama.Da haka zakiga ya zame masu jiki sun saba,
.
Duk inda suka je sai sunyi sallama zasu shiga.
.
zakiga duk gidan da yaranki suka je ana yabawa tarbiy yanki.
.
Anan zamu kwana muna rakon Allah yabamu ikon tarbiyyantar da yaranmu.



MUKYAUTATA IBADUNMU.
.
Kamar koda yaushe shirin yana kara tunatar damu a kan yanda zamu gyara ibadunmu ta
kowane bangare,Annabi (s.a.w) yace, inayi maku wasiyya da kuyi riko da abu ukku
.
Nafarko sallar wutiri kafin kwanciya bacci
.
Nabiyu yin sallar walha akowace ranan.
.
Na ukku yin azumi 3 acikin wata daya wato
13-14-15.
.
Ya Allah kabamu ikon aikata wan nan wasiyyoyin manzon Allah (s.a.w.) .Ummi
Ahmad.



**KIS-SOSHIN ANNABAWA Kashi na 01**

Assalamu Alaikum InshaAllah ayau zan fara gabatar da shiri na mai suna a sama In da yau. Zamu fara da kissar Annabi Adam (As) kamar yadda muka riga muka sani ne cewa a cikin Alkur'ani mai girma cikin surori daban daban wadanda sukayi magana a kan ainihin yadda ubangiji Allah subhanahu wata'ala ya mana ta yadda ya halicci Annabi Adam (AS).

Allah (SWA) ya halicci Annabi Adam(AS) daga wani jinsi Wanda mu yan Adam muke Rayuwa akanta (wato kasa),Wanda akanta muke Rayuwa kuma a cikinta za'a binne mu, kuma a kanta za'a tashe mu.

Kamar yadda yazo a cikin Alkur'ani mai girma, inda Allah (SWA) yake cewa kamar haka-

"Hakika mune muka Halicci mutum daga kekasasshen Dallakin yumbu Abin Cudanyawa".

Ance yayin da Allah (SWT) yayi nufin zai halicci Annabi Adam (AS)Allah ya yiwa kasa wahayi da cewa hakika nizan halicci wata halitta daga yumbun ki, daga cikin wannan halitta akwai Wanda zai bini sannan kuma daga cikinsu akwai wanda zai saba Mani, wanda ya bini zan shigar dashi Aljannah, Wanda kuma ya saba mani zan shigar dashi wuta.

Anan zandakata sai wani lokaci zanci gaba in shaa Allah.



**KISSOSHIN ANNABAWA Kashi 02**

Ayau inshaa Allah zanci gaba daga inda muka kwana,

Sannan sai Allah s.w.t. ya umarci mala'ika jibrilu A.s. daya sauka izuwa kasa, domin ya damki wani sashi na kasa, to a lokacin da mala'ika jibrilu A.s. ya sauko gareta, domain dibar wannan kasa sai kuwa wannan kasa ta fara yi masa magiya da Allah s.w.a. tana mai cewa, hakika ni ina neman tsari da buwayar ubangijin nan da ya aiko ka, akan kada ka debi komai daga gareni, Wanda har ya kasance daga karshe zai zama wani rabo a cikin wuta, jin wannan magiya da mala'ika jibrilu A.s. yayi sai ya kyaleta ya fasa damkar komai daga gareta. Anan zandakata sai wani makon in shaa Allah daga yar'uwarku Hafsat Ahmad Ummi.



KISSOSHIN ANNABAWA
VOL 3 NA IBN ADAM FAGGE.

Har yanzu muna cikin kissar Annabi Adam.mun tsaya inda mala'ika jibril A.s. yakoma zuwa ga Ubangiji s.w.a yace ya Ubangiji hakika wannan kasa tayi mani magiya da cewa kada in debeta, nikuma sai na kasa diban wani abu daga gareta, to sai ubangiji s.w.a. ya kuma umartar mala'ika mika'ilu A.s. akan cewa yaje domin ya damko wani sashi daga gareta,

Yana zuwa sai shima ta fara yi masa magiya da Allah, irin wadda tayi wa mala'ika jibrilu A.s. sai shima yafasa diban komai daga gareta ya koma ya zuwa ga ubangiji s.w.a. ya gaya masa irin magiyar da tayi wa mala'ika jibrilu A.s. sai ubangiji ya kuma umartar mala'ikan mutuwa da yaje ya damko wani sashi daga gareta, sai ya sauko ya zuwa gareta, kafin ta yi masa magiya sai kawai yasa wani mashi ya caketa dashi, jin wannan cakar da yayi mata sai datayi wata irin girgiza sannan ya mika hannu domin ya daibi wani abu daga gareta, ganin haka da tayi sai shima ta fara yi masa magiya irin wadda tayiwa yan'uwansa, sai ya ce mata ai bin umarnin ubangijina yafi magiyar da zaki yi min, sai kawai yasa hannu ya damko daga gareta, har damka(4).

Anan zandakata daga yar'uwarku Hafsat Ahmad Ummi.



KISSOSHIN ANNABAWA
VOL 4 LITTAFIN IBN ADAM FAGGE.

Haryanzu dai muna cikin kissar Annabi Adam A.S.Munkwana a inda mala'ikan mutuwa ya damko kasa ×4 a damkar farko ya damka ta farko ya damki bakar kasa, adamka ta biyu ya damki farar kasa, a damka ta uku ya damki jar kasa mai taushi da duwatsu,

Madaukakanta da makaskantanta, sannan sai yatafi da ita izuwa ga ubangiji s.w.t.
To yana zuwa da ita sai ubangiji s w.t yace dashi, meyasa dakaje zaka damkota tayi maka magiya ba ka kyale ta ba? Sai mala'ikan mutuwa yace masa, ya Ubangiji ai umarninka yafi, sai Allah s.w.t yace dashi daga yanzu Kaine mala'ikan mutuwa mai karban rayukan bayi, to ance wannan wuri da mala'ikan mutuwa ya damka, sai yakama kuka, sai Allah s.w.t yayi mata wahayi da cewa, da sannu za'a komo miki da abinda a ka damko daga gareki, wannan shine fadin Ubangiji s.w.a kamar yanda yazo cikin Alkur'ani mai girma

"DAGA KASA MUKA HALICCEKU, A KUMA CIKINTA ZAMU MAI DAKU, DAGA CIKINTA NE ZAMU FITO DAKU A WANI ZAMANI NA DABAN".

Sannan sai Allah s.w.a ya umarci mala'ikan mutuwa daya ajiye wannan kasar da ya damko a bakin Kofar gidan aljannah, a lokacin daya ajiye ta, sai kuma Allah s.w.t ya umarci mala'ika Ridwanu wato mai tsaron gidan Aljannah, daya dauki wannan kasa ya kwaba ta da ruwan tasnimu.

Anan zandakata sai Allah s w.t yasake hadamu.


KISSOSHIN ANNABAWA Kashi na 5 Daga Littafin IBN ADAM FaGGE,

Haryanzu muna cikin kissar Annabi Adam.
Ubangiji s.w.t. ya kuma umartar mala'ika jibril A.s. daya koma ya kuma debo wata farar kasa, wadda itace zuciyar kasa gaba daya, ance da wannan kasarce aka halicci Annabawa, to sannan sai aka kwaba wannan kasa da ruwa, har sai da wannan kasa ta zama kwababben yumbu mai daraja to sannan bayan an kwaba sai aka barta har sai da takai tsawon shekara 40, sannan ta zamo dallakin yumbu mai danko danko, sannan aka sake barinta ta kuma kaiwa tsawon shekara 40, a nan ma sai da ta zama kekasasshen yumbu mai amo kamar kasko, to a sannan ne aka suranta gangar jikim Dan Adam dashi wannan kwababben yumbun, aka kwantar dashi akan hanyar da mala'iku suke sauko wa, shima aka barshi anan har tsawon shekara 40, batare da an busa masa rai ba.

Kamar yadda Allah s.w.t. ya bayyana mana a cikin Aqur'ani mai girma, kamar haka:-

''LALLAI TSAWON ZAMANI YA ZOWA MUTUM ALHALIN BAI KASANCE KOMAI ABIN TUNAWA BA''

Ance wannan tsawon zamani da ake nufi shine shekara 40, Annabi Adam A.S. yana kwance ba'a waiga izuwa gareshi ba.

Ance bayan Allah s.w.t. yasa ankwaba wannan yumbu na halittar Annabi Adam A.s. sai aka hada wani girgije aka yiwa wannan yumbun ruwan bakin ciki dana bacin rai, har tsawon shekara 40 sannan kuma akayi masa ruwan farin ciki da nishadi na tsawon shekara 1 tak, saboda haka sai bakin ciki dan Adam yafi farin cikinsa yawa, sannan kuma bacin ransa yafi nishadinsa yawa. Baya ga wannan sai Allah s.w.t. ya bayyanar wa da Annabi Adam AS. Jijiyoyin dari ukku da sittin 360. Sannan kuma ya halittar masa gabobi guda 40. Kuma yayi masa mahadar gwiwa guda 12, a cikin kansa kuma yasa masa wasu kofofi 7 sune kamar haka, kunnuwa 2 idanuwa 2 hanci 2 dakuma sannan ya sanya masa hannaye da kafafuwa, da sauran abubuwa ya kuma kammala halittarsa cikakkiyar halitta,

Madalla da ubangiji Wanda yafi kowa iya halitta.anan zamu kwana sai Allah yasake sadamu.

Ummi Ahamd,




Koma saman shafi

→Labarai
1234...9899100»

Share|

Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 1


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake

Adadin Maziyarta 242354

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54


Follow @bjournalist55
→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP
→Home

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358